Hasashen Hisabi icon

Hasashen Hisabi

Rayyahee
$0.99
100+ downloads

About Hasashen Hisabi

An kirkiri wanna Manhajan ne domin ya saukake wa mutane yin Istihara ko bincike ta hanyan hisabi, Kowani mutum zai iya yin Istihara ko bincike da kanshi da wannan Manhajan ko da bai san komai dangane da ilimin hisabi ko taurari ba, abun da yake bukata kawai shine sanin sunayen wadanda zai yi istiharan ko binciken a kansu, da zaran ya shigar da sunayen Manhajar zata fitar mishi da jawabin abin da yayi bincike a kanshi.

Bincike ko Istihara ta hanyan hisabi yana da babobi da yawa domin kowani abu ko kuma kowani matsalan da ya shafi dan Adam za'a iya yin bincike a kanshi domin a gano yanda abun zai kaya, amma a wannan Manhajan mun zabi wasu matsaloli guda bakwai wadanda sune mafiya yawan abubuwan da ke damun al'umma, mu ka fitar da hisabinsu. ga jerin matsalolin nan kamar haka :-


Hisabin Dacewan Soyayya Da Aure

Wannan babin ana amfani da shi ne domin a gano shin Aure tsakanin wane da wacce akwai alhairi ko albarka, kuma za'a ji dadin zamantakewa, sannan za'a iya gane shin auren zai daure ko kuma karshe rabuwa za'a yi tare da nadama. Gane hakan yana da amfani domin mutum ya san irin wanda zai aura kar daga karshe yayi da na sani.

Hisabin Dacewan Mu'amula

Wannan zai taimaka wajen sanin hulda ko mu'amula da wane ko wacce akwai alhairi da nasara.

Hisabin Fahimtan Juna

Wannan zai taimakeka wajen gane ko za'a samu fahimtan juna tsakanin ka da wata ko wani, ko tsakanin wani da wata ko da wani,

Hisabin Mai Ciki

Ana amfani da wannan babin ne domin a gano Namiji ko Mace ko 'yan biyu mai ciki zata haifa, kuma idan cikin zai bare ne, shima zai iya maka bayani.

Hisabin Mara Lafiya

Ana amfani da wannan babin ne domin gano shin mutumin da yake mawuyacin hali na rashin lafiya zai warke ko mutuwa zai yi.

Hisabin Biyan Bukata

Wannan babin zai taimake ka wajen sanin shin zaka samu biyan bukata daga wajen wane ko kuma zai cika alkawarin da yayi maka.

Hisabin Bacewa
Domin gano mutumin da ya bace ko aka sace yana raye ko ya mutu.

Hasashen Hisabi Screenshots